Taro kan makomar kudin CFA Kamaru

Takardun kudin CFA na kasashen renon Faransa
Takardun kudin CFA na kasashen renon Faransa AFP

Shugabannin kasashen tsakiyar Africa shida na halartan babban taron kungiyar CEMAC, a Younde babban birnin kasar Kamaru da zimmar duba alfanun amfani da kudaden CFA, a dai-dai lokaci da kudaden CFA ke neman shiga wani yanayi da bukatar samun murya guda daga kasashen dake amfani da kudaden.

Talla

Taron da ke gudana karkashin jagorancin mai masaukin baki shugaban kasar Kamaru Paul Biya, ya samu halarcin wakilan kungiyar CEMAC, wato shugabannin   kasashen Chadi, da Janhuriyar Tsakiyar Africa, da Equitorial Guinea da Gabon da Jamhuriyar Dimokradiyar Congo.

Biyar daga shugabannin kasashen dai sun halarci taron da kansu, yayinda kasar Gabon wadda shugaban kasar Ali Bango ke fama da lalurar shanyewar jiki ya aika Franministan kasar.

Kasancewar kasashen na da wakilci a kungiyar kasuwanci da tattalin arziki na tsakiyar Africa CEMAC, na amfani da kudaden CFA ne, takardun kudaden da suka gada daga Faransa data mulkesu a yammaci da tsakiyar Africa.

Taro zai tattauna kan takardun kudade na CFA don sanin yadda makomar ci gaba da amfani da shi zai kasance.

Tun ranar 26 ga watan Disamba na shekarar 1945 aka kaddamar da fara amfani da kudaden CFA a Afrika, inda ake da jimillan mutane miliyan 155 a kasashen dake mu'amulla da kudaden.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.