Afrika

Mutane 39 ne suka mutu a Kenya da Tanzania sanadiyar ruwan sama

Ruwan sama  a wasu yankuna
Ruwan sama a wasu yankuna AFP PHOTO / PROSPERT YAKA

Ruwan sama kamar da bakin kwarya mai dauke da iska yayi sanadiyar hallaka mutane 39 a kasashen Kenya da Tanzania.

Talla

Rahotanni sun ce ruwan ya haifar da zabtarewar kasa da kuma rusa gidaje, abinda ya kai ga birne mutane 29 a Kenya, yayin da kogi kuma ya tafi da mutane 10 a Tanzania.

Ministan cikin gidan Kenya, Fred Matiang’i yace mutane 12 sun mutu ne a Tapach da Parua dake kudancin Pokot, yayin da 17 suka mutu a Tamkal dake tsaiyar Pokot.

Tuni aka tura sojoji da yan Sanda domin gudanar da aikin agaji.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.