Buhari ya bada umurnin kammala kamfanin Ajaokuta
Wallafawa ranar:
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya baiwa ma’aikatar ma’adinan kasar umurnin tabbatar da gaggauta kammala aikin gina kamfanin samar da karafan Ajaokuta wanda ake saran ya taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar.
Ministan kula da ma’adinai da kuma karafa Olamikekan Adegbite ya sanar da haka, inda yake cewa tuni ma’aikatar ta tashi tsaye wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar.
Adegbite yace a cikin watanni 3 da suka gabata, ma’aikatar sa ta mayar da hankali wajen ganin an samu cigaba a aikin gina kamfanin kamar yadda shugaban kasa ya bada umurni.
Ana saran dubban mutane sun samu aikin yi bayan kammala gina kamfanin, matakin da zai baiwa Najeriya damar kara yawan kudaden shigar da take samu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu