Burkina Faso

An gano ma'aikata da suka bace a Burkina Faso

Daya daga cikin motocin sojin Burkina Faso dake sunturi a wani yankin arewacin kasar
Daya daga cikin motocin sojin Burkina Faso dake sunturi a wani yankin arewacin kasar MICHELE CATTANI / AFP

A Burkina Faso ,hukumomin kasar sun sanar da gano mutane hudu da ake zaton an yi awon gaba da su,bayan da aka gano motar su a wani yanki dake kudu maso yammacin kasar a marecen jiya.

Talla

Mutanen dake aiki da kamfanin sadarwa na Backbone na kasar sun hada da wasu yan Burkina faso uku da wani dan yankin Asiya.

Gwamnatin Burkina Faso ta cimma yarjejeniya da kamfanin kasar China na Huawei wajen fadada hanyoyin sadarwa a fadin kasar, wanda hakan ke sa wasu daga cikin ma’aikantan kamfanin isa yankuna dake tattare da hatsarin gaske.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI