Matsalar kashe jakuna ta zama babbar barazana ga yawan jakuna da ake dasu a Duniya inda masana ke cewa idan ba’a dauki matakin da ya dace ba, ana iya rasa kusan rabi na jakunan nan da shekaru 5. Wannan na zuwa a dai-dai lokacin da Najeriya ke shirin yin doka kan haramta kashe jakuna, yayin da kungiya mai suna Donkey Sanctuary ta kaddamar da rahoto kan hakan a Abuja dake Najeriya. A cikin shirin Bashir Ibrahim Idris ya duba irin matsalolin da ake fuskanta a wasu yankunan kasashen Afrika.
Sauran kashi-kashi
-
Muhallinka Rayuwarka Matsalar bacewar wasu nau'in itatuwa a yankunan mu A cikin shirin muhalinka rayuwar ka Nasiru Sani ya mayar da hankali a kan daya daga cikin matsaloli na bacewar iatatuwa a wasu yankuna,al'amarin da ya kai hukumomi daukar mataki na samar da shirin sake shuka irin wadanan uiatce tare da goyan bayan kungiyoyi.Nasiru Sani ya jiyo ta bakin masana da masu ruwa da tsaki dangane da wannan matsala.20/05/2023 21:30
-
Muhallinka Rayuwarka MDD- Kudin da ake kashewa wajen sayen ruwan roba ya kai ayi amfani dasu wajen samar da ruwan sha A wannan shirin na Muhallin ka Rayuwar ka, shirin dake tattauna wa da masu ruwa da tsaki kan sauyi ko dumamar yanayi da kuma uwa uba fannin noma da kiwo, wanda Nasiru Sani ke jagoranta.Shirin na wannan mako zaiyi dubi ne kan wani rahoto da Majalisar dinkin duniya ta bayana cewar kudin da ake kashewa wajen sayen ruwan roba ya kai ayi amfani dasu wajen samar da wadataccen ruwan sha a fanfunan daukacin al’uma a duniya.13/05/2023 19:39
-
Muhallinka Rayuwarka Rahoton hadin-gwiwar kungiyoyin manoman Najeriya dake gargadi kan yawan amfanin gonar da ake sacewa Shirin namu a wannan makon, zai duba rahoton hadin-gwiwar kungiyoyin manoman Najeriya dake gargadi kan yawan amfanin gonar da ake sacewa musamman a gonakin arewacin kasar a daidai wannan lokacin na girbi, satar hatsin da rahoton ke cewa zai shafi girbin bana ta fannin karanci da tsadar cimmaka.29/10/2022 19:47
-
Muhallinka Rayuwarka Yadda shaye-shaye ke taka rawa wajen gurbata muhalli Shirin Muhallinka tare da Nasiru Sani ya duba yadda ta'ammali da miyagun kwayoyi ke taka rawa sosai wajen gurbata muhalliu, kamar yadda binciken masana ya tabbatar.22/10/2022 20:02
-
Muhallinka Rayuwarka Kasashen Afirka ta yamma da Sahel za su fuskanci ruwan sama da ambaliya(masana) Kasashen da dama a Afirka ta yamma da na Sahel za su fuskanci ruwan sama masu yawan gaske da ambaliya ,wannan hasashe daga masana na zuwa a dai-dai lokacin da ake kawo karshen taron hukumar kulla da yanayi na kasa a Najeriya Nimet a Abuja.Nasiru sani ya samu tattaunawa da masana dangane da wannan hasashe a cikin shirin Muhalinka rayuwarka daga Rfi.24/07/2022 20:05