Afrika

Mutane 24 sun mutu a wani hatsarin jirgin sama a Goma

Jirgin da ya yi hatsari a wata unguwar Goma na kasar Congo
Jirgin da ya yi hatsari a wata unguwar Goma na kasar Congo AFP Photos/Pamela Tulizo

Akalla mutane 24 ne aka tabbatar da sun mutu sanadiyar hatsarin jirgin sama a garin Goma na Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Talla

Joseph Makundi shugaban hukumar kare hadura a yankin na Goma ya sheidawa kamfanin dilancin labaren Farnsa na AFP cewa wani dan karamin jirgin Fasinjoji na kamfanin Busy Bee dauke da fasinjoji 19 ya kuma rufta saman wani gida cikin wata ungunwa.

Jirgin na daukar dawainiyar jigilar fasinjoji ne daga garin na Beni zuwa Butenbo mai nisan kilometa 350 a arewacin Goma.

Binciken farko na nuna cewa matukin jirgin ne ya hadasa wannan hatsari,biyo bayan rashin samu nasarar cirawa a lokacin da ya dace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI