Nijar

'Yan ta'adda sun kashe masu ungwanni 5 cikin kwanaki 3 a Nijar

Misalin 'yan ta'adda da ke aikata danyen aiki.
Misalin 'yan ta'adda da ke aikata danyen aiki. Daily Post

Masu ungwanni biyar ne ake zargi ‘yan ta’adda sun kashe cikin kwanaki 3 a kudu maso yammacin Niger, kusa da iyaka da Mali.

Talla

Wani dan majalisa daga jihar Tillaberi da bai so a bayyana sunansa bay a shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa daga ranar Alhamis zuwa Asabar aka kashe wadannan masu ungwannin.

An sace mutane 3 har ma da masu unguwanni da ba a tantance adadinsu ba a wasu kauyukan yankin.

A ranar 13 ga watan Nuwamba ma an kashe mai unguwar kauyen Bono, a Tillaberi, bayan an sace shi.

Tsakanin watan Afrilu da Yuli, an kashe akalla wasu masu ungwanni 3, da jami’en Tuareg 4 a harin da aka alakanta da kungiyar IS.

Kauyukan da suka sha wadannan hare – hare na wannan mako suna kusa da kauyen Tongo Tongo, kusa da iyaka da Mali, inda mayakan IS suka taba yin kwanton bauna har suka kashe dakarun Amurka 4 da na Nijar 4 a shekarar 2017.

Hare – haren ‘yan ta’adda sun tilasta wa dubban mutane barin kauyukan su zuwa kudancin kasar ta Nijar.

A karshen watan Oktoba, hukumar ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane dubu 78 ne wannan al’amari ya daidaita a yammacin Tillaberi da Tahoua.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI