Najeriya

Najeriya za ta kaddamar da kundin ajiyar sunayen masu cin zarafin mata

Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari REUTERS/Siphiwe Sibeko

Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani kundin da za’a rika sanya sunayen mutanen da suka aikata laifukan da suka shafi cin zarafin mata da kuma fyade, bayan kotuna sun yanke musu hukunci.Ana saran wannan mataki ya bada damar sanin masu aikata irin wannan laifi duk inda suka shiga, da zummar taka musu birki.

Talla

Wannan kundin zai kunshi sunayen wadanda aka yanke wa hukunci sakamakon aikata laifin cin zarafi ne tun daga shekarar 2015, a wannan kasa da ta fi kowanne yawan al’umma a nahiyar Afrika.

Za a sanya wannan kundi a intanet don amfanin al’umma, hukumomi da ‘yan sanda don binciken gano wadanda suka yi kunnen kashi daga cikin su, suka sake aikata laifin.

Su ma wadanda aka zarga da laifin aikata fyade, amma aka wanke su daga bisani, za a sanya sunayensu a wani kundi da hukumomi ne kawai ke da damar dubawa, lamarin da ya sa masu rajin kare hakkin wadanda aka ci zarafinsu ke korafi, ganin cewa da dama daga cikin masu aikata irin wannan laifi ba sa samun hukuncin da ya dace saboda raunin da bangaren shari’ar kasar ke da shi.

Ko wane dan Najeriya zai samu damar duba wannan kundi da ke karkashin kulawar hukumar yaki da fataucin bil adama, NAPTIP, mai samun tallafin Tarayyar Turai.

A cewar hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya, daya daga cikin 4 na matan Najeriya na fuskantar cin zarafi kafin su kai shekaru 18, kuma yawancin masu laifin ba sa fuskantar hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI