Najeriya

An sake kama masu satar yara a Anambra

Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya Muhammad Adamu
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya Muhammad Adamu NAN

Rundunar 'yan Sandan Najeriya ta sanar da ceto wasu jarirai guda biyu da kananan yara 3 da tace an sace su, inda ta kama mutane biyu da ake zargin suna da hannu a ciki.

Talla

Rundunar tace an kama wadanda ake zargin ne, wadanda mata ne guda biyu, a karamar hukumar Idemili ta Arewa da misalin karfe 1.30 na rana a ranar Alhamis da ta gabata.

Kakakin Yan Sandan Haruna Muhammed ya ce binciken farko da jami’an 'yan Sandan suka yi a ofishin su da ke Otoucha ya bayyana cewar an sato yaran ne daga Enuguwu Aguleri dake Anambra ta Gabas daga hannun wata da ake kira Ani Chisom mai shekaru 28 mazauniyar karamar hukumar Nkanu ta Gabas dake Jihar Enugu, sai kuma Afamefuna Udodili mai shekaru 32 dake Orodo a karamar hukumar Mbaitolu a Jihar Imo.

Mohammed ya ce bayan sanarwar da suka yi, iyayen yaran da aka sace, sun gabatar da kan su, kuma bayan tantancewa an mika musu su.

Jami’in ya ce hukumar 'yan Sandan zata gabatar da wadanda ake zargi a kotu domin hukunta su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI