Mahammadou Salissou Habi kan rufe iyakokin Najeriya

Sauti 03:33
Nigerien information minister, Mahammadou Salissou Habi
Nigerien information minister, Mahammadou Salissou Habi Onep

Gwamnatin Najeriya ta ce har yanzu Jamhuriyar Benin da kuma jamhuriyar Nijar ba su cika sharuddan da kasar ta gindaya musu kafin bude iyakarta da wadannan kasashe ba. Ministan Yada Labaran Najeriya Lai Mohammed, ya ce ko a cikin makonni biyun da suka gabata, jami’an tsaron kasar sun kama haramtattun kayayyakin da aka kiyasta cewa kimarsu ta kai Naira bilyan 35 a kan wadannan iyakoki. To sai dai Ministan Yada Labaran Jamhuriyar Nijar Mahammadou Salissou Habi ya ce gaskiya kasar ta damu da matakin ci gaba da rufe iyakar da Najeriya ta dauka.