Najeriya

Nijar da Benin ne suka hana mu bode iyakarmu- Najeriya

Wani bangare na kan iyakar Najeriya da Nijar
Wani bangare na kan iyakar Najeriya da Nijar BOUREIMA HAMA / AFP

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ce, kamen da jami’an tsaronta suka yi na dimbin kayayyakin fasa kauri akan iyakokin kasar, alama ce da ke nuna cewa, har yanzu, kasashen Nijar da Benin sun gaza magance matsalolin da suka tilasta mata rufe iyakokinta.

Talla

Ministan Yada Labarai da Al’adu na Najeriya, Lai Mohammed ya bayyana haka a yayin wata ziyara da ya jagoranci tawagar kasar zuwa kan iyakar Seme a ranar Litinin.

Ministan ya ce, kawo yanzu, an kama mutane 296 da suka shigo Najeriya ta haramtacciyar hanya, yayin da kuma aka kwace wasu tarin kayayyakin da aka yi fasa kaurinsu da suka hada da buhunan shinkafar waje mai nauyin Kilogram 50 har guda dubu 38, 743.

Kazalika jami’an na Najeriya sun yi nasarar kwace motoci 514 da gangunan man fetur 1,012 da jarkokin man kyada 5, 400, baya ga babura 346 da kuma buhuna 136 na takin NPK da ake amfani da su wajen kera abubuwan fashewa.

An kiyasta cewa, kudaden wadannan kayayyakin da aka kama, sun kai Naira biliyan 3.5.

Ministan ta zargi Jamhuriyar Benin da shirin shigo da shinkafar da kudinta ya kai Dala miliyan 30 cikiin Najeriya.

Kazalika ya zargi Benin da Nijar da gazawa wajen mutunta ka’idojin da Kungiyar ECOWAS ta shinfida na safarar kayayyaki tsakanin kasa da kasa, yana mai cewa kasashen biyu na cusa wasu haramtattun kaya cikin sundukan da ake balaguron su zuwa Najeriya daga can wasu kasashen waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI