Isa ga babban shafi
Faransa-Mali

An gano akwatunan nadar bayanai jiragen sojin Faransa da suka yi hatsari a Mali

Hotunan wasu daga cikin dakarun Faransa
Hotunan wasu daga cikin dakarun Faransa JEFF PACHOUD / AFP
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
1 Minti

Rundunar sojin Faransa ta ce an gano akwatunan nadar bayanai na jiragen sojin da suka yi taho mu gana a yankin Liptako da ke daf da iyakar Mali, Nijar da kuma Burkina Faso.A ranar litinin da ta gabata ne wannan hatsari ya faru, a daidai lokacin da dakarun saman Faransa ke farmaki kan yan ta’adda a yankin na Liptako. To sai dai gano wadannan akwatunan zai taimaka domin sanin hakikanin abin da ya haddasa mutuwar sojojin 13.

Talla

Fadar shugaban Faransa ta ce an samu hadarin ne lokacin da jiragen biyu masu saukar ungulu suka yi taho mu gama a tsakanin su.

Wannan shi ne hadari mafi muni da sojojin Faransa suka gamu da shi tun bayan hadarin bama-baman Lebanon na shekarar 1983 wanda ya hallaka mutane 58.

Shugaba Emmanuel Macron ya bayyana kaduwar sa da hadarin wanda ya hada da hafsoshi guda 6 da wadanda ba hafsoshi ba guda 6 da kuma kofur guda da ke aikin yaki da 'yan ta’adda a Sahel.

Ministar tsaro Florence Parly ta ce hadarin ya girgiza rundunar sojin da ma’aikatar tsaro da kasar Faransa baki daya, yayin da ta ce za’a kaddamar da bincike akai domin gano abinda ya yi sanadinsa.

Cikin wadanda hadarin ya ritsa da su harda ‘dan tsohon minista kuma Sanata Jean-Marie Bockel.

Bakwai daga cikin sojojin na aiki ne da runduna ta 5 da ke yaki da jiragen shalkwafta a Pau da ke Faransa, yayin da 4 kuma ke karkashin dakarun Gap.

Gwamnatin Faransa zata gudanar da addu'o'i a fadin kasar ranar litinin mako na sama ,yayinda aka bayyana cewa Ministar tsaron kasar Florence Parly zata kai ziyara kasar Mali nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.