Najeriya

Rufe iyakoki ya janyo kuncin rayuwa - Najeriya

Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya.
Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya. ng.gov.jpg

Gwamnatin Tarayyar Najeriyata ce lallai ana iya danganta matsalar hauhawar farashin kayayyaki da rufe kan iyakokin kasar da ta yi.

Talla

Ministar kudi da tsare – tsaren kasar, Hajiya Zainab Ahmed ce ta bayyana haka a Abuja, bayan taron majalisar zartaswar kasar, wanda shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta.

Hajiya Ahmed ta ce rufe kan iyakokin ba na dindindin ba ne, kuma za a sake budewa saboda tattaunawa tsakanin kasashen da ke makwaftaka da Najeriya ta yi nisa.

Ministar ta ce gwamnatin kasar na fatan tattaunawar ta taho da sakamako mai armashi, kuma yarjejeniyar da za a cimma za ta sa kasashen da abin ya shafa su mutunta ka’idoji har a sake bude kan iyakokin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI