Najeriya

Najeriya ta jinginar da dala miliyan 200 don ceto kadarorinta

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari. REUTERS/Dan Kitwood

Gwamnatin Najeriya ta bayar da jinginar dalar Amurka milyan 200 a gaban wata kotun Birtaniya, domin hana wasu kamfanoni kwace kadarorinta da kimarsu ta kai dala biliyan 9; kudaden da ta yi alkawarin biyan wadannan kudade a cikin kwanaki 60 masu zuwa.

Talla

Gwamnatin Najeriya ta biya wadannan kudade ne a matsayin jingina, domin samun damar daukaka kara a wannan takun-saka da ke tsakaninta da wani kamfani mai suna Industrial Development Limited, wanda aka bai wa kwangilar hako iskar gas a shekara ta 2010.

An samu sabani tsakanin gwamnatin Najeriya da wannan kamfani ne har aka kwace wannan kwangila, daga nan ne kuma sai kamfanin ya shigar da kara a gaban kotun Birtaniya domin a biya shi diyyar dala bilyan 9.

A watan Agustan da ya gabata ne alkalin wata kotun a kasar ta Birtaniya, ya bayar da umarnin kwace kadarorin Najeriya da suka kai dala biliyan 9, wato kimanin kashi 1 cikin 5 na kudaden a asusun ajiyar kasar da ke ketare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI