Afrika

Chadi na shirin aikewa da sojoji kan iyakokin kasar

Shugaban Chadi Idriss Déby, na Nijar  Mahamadou Issoufou da Burkina Faso  Roch Marc Christian Kaboré a taron kungiyar Ecowas
Shugaban Chadi Idriss Déby, na Nijar Mahamadou Issoufou da Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré a taron kungiyar Ecowas ISSOUF SANOGO / AFP

Kasar Chadi na nazarin sake aikewa da sojoji zuwa iyakokin kasar da Nijar, Burkina Faso da Mali.Matakin da akasarin magoya bayan Shugaban kasar a zauren Majalisa ke nazari a kai.

Talla

Ana sa ran magoya bayan Shugaban kasar za su mika wuya don ganin Chadi ta tura da sojoji kamar dai yada ta yi a baya zuwa wadanan yankuna, matakin da yayi tasiri a baya.

Daya daga cikin memba a jam’iyya mai mulkin kasar Jean Bernard Padare mudin Chadi ta kawar da idanu dangane da wadanan matsaloli da suka jibanci tsaro, kasar za ta iya samun kan ta a cikin wani yanayi na rashin tsaro a nan gaba, ya zama wajibi kasar ta dau matakan da suka dace don kare kan iyakokin ta da sauren aminan ta.

Baya ga kasar ta Chadi kasashen Nijar ,Mali ,Burkina Faso na fama da rashin tsaro ,lamarin da ya tilastawa da dama daga cikin jama’a tserewa zuwa wasu yankuna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI