Afrika

Majalisar Dinkin Duniya ta damu da halin da ake ciki a Beni

Jean-Pierre Lacroix a garin Beni na jamhuriyar demokradiyyar  Congo
Jean-Pierre Lacroix a garin Beni na jamhuriyar demokradiyyar Congo robert minangoy <africa1minangoy@yahoo.fr>, hausa conductor <rfi

Mataimakin Sakatary Majalisar Dinkin Duniya Jean Pierre Lacroix ya kai ziyara garin Beni dake Jamhuriyar Demokradiyyar Congo a yau asabar.Wanan yankin ya kasance daya daga cikin yankunan da aka fi samu mutuwar farraren hula a dan tsakanin nan a kasar.

Talla

A makon da ya gabata ne yan bindiga suka kai wasu jerry hare-hare zuwa jama’a a garin na Beni.

Rahotanni baya-bayan nan na nuni cewa akala mutane 100 yan tawaye a dan tsakanin nan suka hallaka su kama daga ranar 5 ga watan Nuwamba.

Jean Pierre Lacroix zai yi amfani da wannan dama domin ganawa da dakarun wanzar da zaman lafiya a yankin na Beni, da kuma ganawa da babban hafsan sojan kasar da shugabanin kabilu dake yankin ga baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI