Afrika

Ana tsare da wasu jami'an gwamnatin Gabon

Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Odinba a birnin Libreville.
Shugaban kasar Gabon Ali Bongo Odinba a birnin Libreville. MIKE HUTCHINGS / POOL / AFP

Manyan jami’an gwamnatin kasar Gabon 21 ne aka cafke sannan aka gurfanar da su a gaban kotu bisa zargin rashawa da kuma handame dukiyar kasar.Bayan sun gurfana a gaban kotu tare da amsa tambayoyi daga alkalai, daga cikin mutanen 21 an sallami 8 yayin da sauran 13 ke ci gaba da kasancewa a hannun jami’an tsaro don yin bincike a kansu.

Talla

A shekarar da ta shude ne shugaban kasar Gabon Ali Bongo ya kori kashi 40 cikin dari na jami’an dake aiki a fadar sa, a wani yunkuri na rage facaka da kudin gwamnati, inda ya kira Ministocinsa da suyi koyi da shi.

Tuni dai matakin ya haifarar da cece-kuce dama fargaba tsakanin jami’an da ke ayyuka karkashin ministocin kasar.

A lokacin wata sanarwa daga majalisar ministoci ta fito da jerin sunayen wasu takaitattun mutane da suka rage a matsayin abokan aikin shugaban kasa, yayinda wadanda ba suga sunayen su ba kuwa zasu koma ma’aikatunsu ta asali.

Rahotanni sun ce shugaban Ali Bongo zai yi aiki ne kadai da kusoshin gwamnatin da suka zame masa wajibi kamar daraktan fadar sa da kuma sakataran gwamnatin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.