Najeriya

Ganduje ya gabatarwa Majalisa bukatar kirkiro sabbin masarautu

Sarkin Kano Alhaji Sunusi Lamido Sunusi tareda Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje
Sarkin Kano Alhaji Sunusi Lamido Sunusi tareda Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje Dandago RFI

Gwamnan Jihar Kano dake Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da wani sabon kudiri a zauren Majalisar dokokin Jihar inda yake bukatar kirkiro sabbin masarautu guda 4.

Talla

Matakin gwamnan na zuwa ne kwanaki bayan kotu ta rusa Masarautu guda 4 da aka kirkiro a Jihar, saboda abinda ta kira saba ka’ida wajen yin dokar kirkiro masarautun.

Kwamishinan yada labaran Jihar, Muhammed Garba yace wasu daga cikin wadannan masarautu da ake bukatar kirkirowa sun ma girmi Masarautar Kano, saboda haka wannan mataki wani yunkuri ne na farfado da su.

Kwamishinan ya kuma ce an yiwa dokar gyara domin dacewa da bukatun jama’a musamman wadanda suka fito daga wadannan yankuna da za’a kirkiro musu.

Masarautun sun hada da na Rano da Gaya da Bichi da kuma Karaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.