Jamhuriyar Benin ta kaddamar da wani gagarumin shirin tantance ‘yan kasar a Najeriya
Gwamnatin Jamhuriyar Benin ta kaddamar da wani gagarumin shirin tantance ‘yan kasar da ke zaune a tarayyar Najeriya.Da jimawa dai ne Jamhuriyar Benin ta shirya gudanar da wannan aiki,wanda zai taimaka don tattance yan kasar ta dake zaune waje tareda basu damar gudanar da harakokin su a tsanake.
Wallafawa ranar:
Benoua Adekambi, mai bai wa ministan harkokin wajen kasar ta Benin shawara ya bayyana cewa babbar manufar wannan shiri ita ce tantance illahirin ‘yan kasar Benin da ke zaune a Najeriya. Abin tuni a nan shi ne, yau kimanin shekara daya da rabi kenan da aka kaddamar da irin wannan aiki a cikin gida Jamhuriyar Benin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu