Burkina Faso

An kashe mutane a harin ta'addanci a Burkina Faso

Sojojin Burkina Faso a yankin Soum
Sojojin Burkina Faso a yankin Soum MICHELE CATTANI / AFP

‘Yan bindiga sun kashe mutane 15 lokacin da suke gudanar da ibada cikin wata mujami’a da ke garin Hantoukuoura jiya lahadi a gabashin gabashin kasar Burkina Faso.

Talla

Bayanai sun ce ‘yan bindiga a kan babura sun kai hari kan wannan mujami’a ta mabiya darikar Protestant ne da ke lardin Foutouri kusa da iyakar kasar da Jamhuriyar Nijar kuma sanarwa da fadar gwamnan lardin Fadan Ngourma ta fitar ta ce mutane 14 ne suka rasa rayukansu a wannan hari.

Hare-haren ta'addaci ya tilastawa da dama daga mazauna yankunan arewacin kasar ficewa daga gidajen su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.