Nijar

Wasu mahara sun kashe yan Sanda biyu a garin Shawagui

Wasu yan bindiga sun hallaka jami’an yan Sanda biyu a garin Shawagui dake da nisan kilometa biyu da garin Dan Kano yankin Tibiri dake Guidam Roumdji.

Wasu daga cikin yankunan dake fama da matsalolin tsaro
Wasu daga cikin yankunan dake fama da matsalolin tsaro Fati Abubakar/RFI
Talla

Maharan sun shigo garin ne da nufin awon gaba da dabobin dake cikin wannan gari, labarin da jami'an tsaro suka samu,kuma nan take aka tura da yan sanda zuwa garin.

A bata kashi da aka yi ne yan sanda biyu suka kwanta dama.

Jami'an tsaron sun samu nasarar kashe wasu daga cikin maharan kamar dai yada rahotanni suka tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI