Afrika

Yan Boko Haram sun kashe sojan Chadi

Wasu yan bindiga da ake kyautata zaton mayakan kungiyar boko Haram ne sun kashe sojojin Chadi guda 4 kusa da wani sabon sansanin su dake Tafkin Chadi.Kamfanin dillancin labaran Faransa yace book haram na da wurin horar da mayakan ta a sassa daban daban na tsibirin, wanda ya ratsa kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da kuma Chadi.

Dakarun dake fada da yan Boko Haram a yankin tafkin Chadi
Dakarun dake fada da yan Boko Haram a yankin tafkin Chadi REUTERS/Warren Strobel
Talla

Wata majiyar soji tace dakarun Chadi sun yi nasarar kasha 13 daga cikin mayakan, yayin da wasu sojojin su 3 suka samu raunuka a wani hari da aka kai litinin da misalign karfe 1 na dare.

Gwamnan Tafkin Chadi, Nouki Charfadine ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yake cewa sun kafa sansanin dake tsakanin Ngouboua da Bagassoula ne saboda satar jama’a da akeyi.

Rahotanni sun ce wasu mazauna kauyuka 5 sun mutu a harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI