Bikin mika takobin jagora Alhaji Umaru Futiyu Tall a birnin Dakar

Sauti 10:00
Takobin jagora Alhaji Umaru Futiyu Tall a birnin Dakar
Takobin jagora Alhaji Umaru Futiyu Tall a birnin Dakar RFI/Charlotte Idrac

A ranar 17 ga watan Nuwambar wannan shekara ta 2019 ne, Firaminista Faransa Edouard Philippe ya mika wa shugaban Senegal Macky Sall takobin Sarki kuma shugaban addini Alhaji Umaru Futiyu Tall, wanda turawan mulkin mallakar Faransa suka kwace sannan suka yi awun gaba da shi a shekara ta 1893.An gudanar da wannan biki ne a birnin Dakar fadar gwmanatin Senegal tare da halartar manyan jami’an gwamnatocin kasashen biyu, ‘yan majalisar dokiki sannan kuma da halartar tawagar zuriyar Sheikh Alhaji Umaru Tall.Mahaman Salisu Hamisu a cikin shirin al'adun mu na gado ya duba mana yada aka gudanar da wannan biki na Dakar.