Bakonmu a Yau

Farfesa Muntaka Usman game da umarnin Kotu na daina biyan tsaffin Gwamnoni Fansho

Wallafawa ranar:

Wata Kotun Tarayya da ke Lagos a Najeriya ta zartas da hukuncin cewa Gwamnatin kasar ta kwato kudaden Fansho da ake baiwa tsaffin Gwamnoni da a yanzu su ke rike da mukamin Ministoci ko kuma wakilai a majalisar kasa. Kazalika Kotun ta umarci Ministan shari'a da ya kalubalanci dalilin da ya sa Gwamnatocin jihohi ke baiwa tsoffin Gwamnoninsu makudan kudade da sunan Fansho.Wannan na biyo bayan takaddamar da aka samu Zamfara inda Gwamnatin yanzu ke biyan kudaden da suka kai Naira Miliyan 700 a shekara ga tsoffin Gwamnonin jihar. Garba Aliyu Zaria ya tuntubi Farfesa Muntaka Usman na Jamiar Ahmadu Bello dake Zaria don jin yadda suke kallon lamarin.

Alamar kotunan Shri'a a Najeriya.
Alamar kotunan Shri'a a Najeriya. The Guardian
Sauran kashi-kashi