Najeriya

Najeriya na dauke da kashi 25 cikin 100 na Malaria- WHO

Samfurin gidan sauro da nufin kariya daga cutar Malaria da sauro ke haddasawa.
Samfurin gidan sauro da nufin kariya daga cutar Malaria da sauro ke haddasawa. www.msf.org

Wani sabon rahoton hukumar lafiya ta duniya WHO ya bayyana cewa, Najeriya ce ta dauki kashi 25 cikin dari na cutar zazzabin cizon sauron da aka yi fama da ita a duniya cikin shekarar 2018.

Talla

Rahoton na WHO wanda hukumar ta fitar a yau Laraba, ya kuma nuna yadda Najeriya ta samu raguwa a yawan cutar Malaria da ta ke fuskanta a cikin shekarar 2018 idan aka kwatanta da shekarun baya.

Rahoton na WHO ya nuna cewa duk da yawaitar adadin wadanda suka kamu da cutar ta Malaria a Najeriya cikin shekarar ta 2018 da ya kai kashi 25 cikin dari na yawan cutar ta zazzabin cizon sauro da ilahirin duniya ta fuskanta, Najeriyar ta yi namijin kokarin wajen rage yawan masu kamuwa da cutar, wanda hukumar ta WHO ke cewa abin maraba ne don ci gaba da yakar cutar ta Malaria.

A cewar rahoton cikin shekarar ta 2018 mutane miliyan 228 ne suka kamu da cutar ta Malaria kasa da adadin da suka kamu a shekarar 2017 na mutane miliyan 231.

Haka zalika WHO cikin rahoton na ta, ta bayyana cewa Najeriya da wasu kasashen Afrika 18 da kuma India ne ke samar da kashi 85 na yawan mutanen da ke kamuwa da cutar ta zazzabin cizon sauro ko kuma Malaria a kowacce shekara.

Acewar hukumar lafiyar ta duniya WHO matakan magance matsalar cutar ta Malaria na matsayin manyan kalubale ga kasashe galibi masu tasowa wanda ke bukatar tallafin kasashe, kungiyoyin lafiya don yakar cutar maimatukar hadari.

Cikin kasashen da WHO ta bayyana cewa Malaria na matsayin babban kalubalen lafiya garesu baya ga Najeriyar akwai Nijar kana Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo sannan Uganda Mozambique da kuma Cote d’Ivoire wadanda hukumar ke cewa suna dauke da kashi 50 cikin dari na Malariar da ke barazana ga duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI