Najeriya

Yan kungiyar IPOB sun kashe matamakin kwamishinan yan Sanda

Rundunar yan Sandan Najeriya ta tabbatar da cewar, yan kungiyar IPOB dake fafutukar kafa kasar Biafra sun kashe mata matamakin kwamishinan yan Sanda da kuma Sufritanda lokacin da suka ke gidan lauyan Nnamdi Kanu, Ifeanyi Ejiofor dake Jihar Anambra.

Nnamdi Kanu Shugaban kungiyar IPOB a  Najeriya
Nnamdi Kanu Shugaban kungiyar IPOB a Najeriya REUTERS/Afolabi Sotunde/Files
Talla

Mai Magana da yawun Yan Sandan yace mataimakin kwamishinan Yan Sandan Oliver Abbey na aiki ne a matsayin kwamnadan shiyar Oraifite, yayin da Sufritanda Joseph Akubo kuma ke aiki da sashen yaki da yan fashi da makami lokacin da suka ziyarci gidan lauyan domin gayyatar sa, abinda ya sa magoya bayan sa suka kai musu harin da ya hallaka su, kana suka kona motocin su.

Sai dai shugaban kungiyar dattawan yan kabilar Igbo, John Nwodo ya bukaci kafa kwamitin bincike kan lamarin, bayan ya zargi jami’an tsaro da amfani da karfin da ya wuce kima.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI