Mauritania

Bakin - haure 58 sun mutu a gabar ruwan Mauritania

Jirgin ruwan kungiyar The Open Arms  mai ceto bakin - haure a teku.
Jirgin ruwan kungiyar The Open Arms mai ceto bakin - haure a teku. REUTERS/Guglielmo Mangiapane

Hukumar kula da bakin – haure ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla bakin 58 suka mutu bayan kwale – kwalen dake dauke da su ya nutse a kusa da gabar ruwan Mauritania bayan sun shafe kusan mako daya suna tafiya a teku.

Talla

A cewar hukumar, wasu bakin – haure 83 sun yi iyo zuwa gabar ruwa, yayin da wadanda suka tsallake rijiya da baya suka ce kimanin mutane 150, ciki har da mata da yara ne ke cikin kwale- kwalen da ya tashi daga Gambia tun ranar 27 ga watan Nuwamba.

Mutanen sun ce mai ya kare wa kwale –kwalen ne yayin da ya doso gabar ruwan Mauritania.

Babbar jami’ar hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya Laura Lungarotti ta ce lallai hukumomi a Mauritania sun dage wajen aikin ceto wadanda suka yi katari, inda take cewa babban abin da ke gaban hukumar shine baiwa wadanda suka tsiran taimakon da suke bukata.

Wata sanarwa daga hukumar kula da bakin – hauren ta ce an garzaya da wadanda ke neman kulawa daga cikin wadanda suka tsiran asibiti a garin Nouadhibou, da ke gabar ruwan Mauritania.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.