Kotu a Senegal ta jefa malamin tsangaya kurkuku
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kotu a Senegal ta yanke wa wani malamin tsangaya hukuncin zaman gidan yari saboda kama shi da laifin azabtar da dalibansa ta hanyar dauresu da sarka. Lamarin da ya janyo mabanbantan ra’ayoyi a kasar dake yammacin Afrika.
A cikin watan da ya gabata ne dai aka tsare malamai 6 bayanda da aka gano dalibai da dama, garkame da sarka a makarantunsu da ke arewacin garin Ndiagne.
Magoya bayan wadannan malaman dai sun yi watsi da hukuncin kotun, inda suka bukaci a tsare 4 daga cikin iyayen daliban tare da makerin da ke kera marin da ake amfani da su wajen daure daliban.
Kashi 90 cikin 100 na Musulman kasar Senegal dai sun dogara da dubban makarantun addini a fadin kasar ta hanyar damka musu amanar tarbiyantar da ‘ya’yansu, sai dai mafi yawa daga cikin makarantun da ba su tanadi kaidoji ba, na amfani da wannan dama wajen azabtar da dalibai.
A cikin watan Yunin da ya gabata, kungiyoyin kare hakkin dan adam sun koka kan yadda ake samun yawaitar cin zarafin alumma, ta hanyar fyade, ke tilastawa dalibai shiga harkar barce - barace, da kuma tsare dalibai a cikin makarantun tsangayan tamkar kurkuku.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu