Najeriya-Boko Haram

Boko Haram ta sace mutane 14 a Maiduguri har da Sojin Najeriya

Shugaban tsagin kungiyar Boko Haram ISWAP da ke biyayya ga kungiyar IS Abu Musab Al-Barnawi
Shugaban tsagin kungiyar Boko Haram ISWAP da ke biyayya ga kungiyar IS Abu Musab Al-Barnawi Guardian Nigeria

Wata majiyar tsaro a Najeriya ta tabbatar da farmakin mayakan jihadi a jihar Borno inda suka yi garkuwa da mutane 14 ciki har da Sajan din Soja guda da jami’an kungiyar bayar da agajin gaggawa ta Red Cross.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa, da ke bayyana labarin ya ce a yammcin ranar laraba ne lamarin ya faru inda mayakan tsagin kungiyar ta Boko Haram da ke wakilcin kungiyar IS a yammcin Afrika ISWAP suka tare kan hanyar da ta sada garin Damaturu da Maiduguri tare da sace mutanen 14.

Majiyar ta tabbatarwa kamfanin cewa cikin wadanda aka sacen har da wani Sajan din Soja da iyalansa baya ga jami’an agaji na kungiyar Red Cross sai kuma karin fararen hula.

Garkuwa da jami’an na Red Cross 2 shi ne farmakin kungiyar ta’addancin na baya-bayan nan da ya ritsa da jami’an agaji.

Sai dai sanarwar tabbacin harin da ISWAP ta fitar a jiya Alhamis ta bayyana cewa tana rike da sojin Najeriyar 6 da kuma fararen hula 8 ciki har da jami’an na Red Cross.

Tun a shekarar 2016 ne kungiyar ta Boko Haram ta rabu gida biyu, inda bangaren Abubakar shekau ya ci gaba da zama a matsayin Boko Haram yayinda bangaren Albarnawi ya koma biyayya ga babbar kungiyar ta’addanci ta duniya IS tare da sauya suna zuwa ISWAP.

A baya-bayan nan kungiyar ta ISWAP c eke kaddamar da manyan hare-hare a yankin arewa maso gabshin Najeriya baya ga garkuwa da mutane da kuma aiwatar da kashe-kashe ciki har da kisan tarin jami’an tsaron hadakar kasashen Najeriya Nijar Kamaru da kuma Chadi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI