Kenya

'Yan sanda sun kama gwamnan da ya sace kudin talakawa

Gwamnan Nairobi da ke Kenya Mike Sonko tare da magoya bayansa
Gwamnan Nairobi da ke Kenya Mike Sonko tare da magoya bayansa REUTERS/Thomas Mukoya

An cafke gwamnan babban birnin Nairobi da ke Kenya bayan mai shigar da kara na gwamnatin kasar ya bada umarnin tsare shi bisa zargin cin hanci da rashawa.

Talla

Gwamna Mike Sonko, shi ne na baya-bayan nan daga cikin jerin manyan jami’an gwamnati da suka hada da Ministan Kudi, Henry Rotch da aka tasa keyarsu saboda zargin cin hanci da rashawa, yayin da gwamnatin kasar ta dukufa wajen yaki da matsalar ta rashawa.

Mai magana da yawun Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kenya, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Faransa cewa, sun cafke gwaman ne a garin Voi da ke yankin kudancin kasar.

Wasu hotuna da aka yada a kafafen sada zumunta, sun nuna gwamnan na takaddama da jami’an ‘yan sanda kafin daga bisani a sanya masa ankwa tare da jefa shi cikin jirgin sama mai saukar ungulu zuwa Nairobi.

Mai shigar da karar na gwamnatin kasar, Noordin Haji ya zargi gwamnan da wasu jami’ai da karkatar da kudaden talakawa domin amfanar da kansu, inda kuma suka biya kansu da kansu Dala miliyan 3.5.

Mai shigar da karar ya ce, yana da cikakkiyar shaidar da ta ba shi damar gurfanar da gwamnan da sauran mukarraban da suka yi tarayya da shi a wannan almundahana.

Gwamna Sonko dai ya shahara musamman ta fuskar ado da kuma nuna kai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.