Gambia

Al'ummar Gambia na makokin 'yan ciraninsu da suka mutu a teku

Wani jirgin 'yan ciranin Gambia.
Wani jirgin 'yan ciranin Gambia. Romain CHANSON / AFPTV / AFP

Dubban jama’ar Gambia ke ci gaba da makokin ‘yan uwansu da suka rasa rayukansu a teku bayan nustewar kwale-kwalen ‘yancirani a Mauritania dauke da tarin mutanen da ke kokarin tsallakawa nahiyar Turai don samun ingantacciyar rayuwa, hadarin da ke matsayin irin mafi muni cikin shekarar nan ga al’ummar yammacin Afrika.

Talla

Akalla mutane 62 aka tabbatar da mutuwarsu a nutsewar kwale-kwalen yayinda wasu da dama kuma aka yi nasarar tsamosu da ransu can a gabar ruwan Mauritania.

Kididdigar da hukumar kula da ‘yan cirani ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar ta bayyana cewa galibin mutanen da suka rasa rayukansu sun fito ne daga kasar Gambia a kokarinsu na tsallakawa Turai, dai dai lokacin da tattalin arzikin kasar ke fuskantar shakar mutuwa.

Ko a jiya Juma’a ma sai da Mahukuntan Mauritania suka sake kame wani jirgi makare da al’ummar Gambia 192 suna kokarin tsallakawa Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.