Najeriya-MDD

Mata dubu dari takwas na fama da yoyon fitsari a Najeriya

Wasu mata da ke gangamin kawo karshen yoyon fitsari a Najeriya
Wasu mata da ke gangamin kawo karshen yoyon fitsari a Najeriya

Hukumar Kula da Yawan jama’a ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce mata 800,000 a Najeriya ke zama da matsalar yoyon fitsari, yayin da a kowace shekara ake samun 20,000 dake kamuwa da matsalar.

Talla

Jami’ar hukumar dake Kaduna, Mariama Darboe ta gabatar da wannan adadi na mata 800,000 da ke dauke da cutar yoyon fitsari a Najeriya, gabanin taron masu ruwa da tsaki kan matsalar da za’a fara ranar 18 ga wannan wata.

Darboe wacce ta bayyana adadin a matsayin mai tada hankali, ta ce ana samun tsakanin sabbin mata 12,000 zuwa 20,000 da suke kamuwa da matasalar kowace shekara.

Jami’ar ta ce taron da za su gudanar zai taimaka wajen janyo hankalin hukumomi da sauran jama’a kan yadda ake kamuwa da cutar wajen gardamar haihuwa, wadda ke jefa dubban mata cikin halin kakanikayi sakamakon rashin sani musamman ga wadanda ke zama a kauyukan da ba’a samun kula da lafiyar su.

Darboe ta ce ana iya magance kamuwa da wannan matsala ta yoyon fitsari idan aka dauki matakan da suka dace ta hanyar jinkirta daukar ciki ga kananan mata da samun kula daga kwararrun masu karbar haihuwa da kuma baiwa matan dake fuskantar matsalar haihuwa kular da ta dace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI