Najeriya

DSS ta musanta sake kame Sowore a cikin Kotu

Hoton da ke nuna yadda jami'an DSS suka sake kame Omoyele Sowore har cikin dakin shari'a na babbar kotun Najeriya.
Hoton da ke nuna yadda jami'an DSS suka sake kame Omoyele Sowore har cikin dakin shari'a na babbar kotun Najeriya. REUTERS/Afolabi Sotunde

Rundunar tsaron farin kaya ta DSS a Najeriya DSS ta musanta sake kame mawallafin jaridar Sahara ta yanar gizo Omoyele Sowore a cikin babbar kotun kasar da ke Abuja, duk kuwa da faifan bidiyon da ke nuna jami’anta na aikata hakan, ranar juma’ar da ta gabata.

Talla

Sowore wanda ya shafe kwanaki 125 hannun jami’an tsaron Najeriyar duk da mabanbantan umarnin Kotu da suka bukaci sakinsa, a ranar Alhamis din da ta gabata ne, rundunar ta DSS ta amsa bukatar kotu tare da sakinsa bayan wani umarni da ya nemi gaggauta sakinsa cikin sa’o’I 24.

Sai dai kuma a ranar juma’ar tarin jami’an na DSS suka dirarwa babban kotun Tarayya da ke birnin Abuja tare da sake kama shi har a cikin dakin shari’a.

Wasu rahotanni na nuni da cewa mahukuntan Najeriyar na zargin Sowore da cin amanar kasa baya ga batanci ga shugaban kasar Muhammadu Buhari.

Cikin sanarwar ta DSS ta fitar ta hannun kakakinta Peter Afunnaya ta musanta cewa har a cikin dakin shari’a na babbar kotun Najeriyar ne ta kame dan gwagwarmayar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.