Kenya

Ana farautar Zakin da ya tsere daga gidan tsare namun daji

Hukumomin kasar Kenya sun yi shelar cewar yanzu haka suna neman wani zaki da ya tsere daga gidan aje namun daji dake birnin Nairobi, bayan ya kubuce ya kuma kashe mutum guda.

Masu tsaron gidan namun daji a Kenya sun kaddamar da farautar Zakin da ya tsere.
Masu tsaron gidan namun daji a Kenya sun kaddamar da farautar Zakin da ya tsere. AFP
Talla

Hukumar kula da gandun dajin kasar tace ta kaddamar da farautar neman zakin wanda tace an masa allurar barci amma hakan bai hana shi tserewa ba.

Sanarwar hukumar tace tana jajantawa iyalan mutumin da zakin ya kashe, yayin da take kuma gargadin jama’ar birnin Nairobi cewar, suyi taka tsan tsan da kuma kaucewa yawon dare yau litinin, har sai an kama zakin.

Ko a shekarar 2016 sanda aka samu irin wannan, inda zakuna sau 4 suna ficewa daga inda ake tsare da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI