Algeria

Kotu ta aike da tsaffin Firaministan Algeria 2 gidan yari

Ahmed Ouyahia guda cikin tsaffin Firaministan Algeria 2 da kotu ta aike gidan yari.
Ahmed Ouyahia guda cikin tsaffin Firaministan Algeria 2 da kotu ta aike gidan yari. Louafi Larbi / Reuters

Kotun Algeria ta aike da tsaffin Firaministan kasar 2 zuwa gidan yari yau Talata bayan samunsu da hannu dumu-dumu a badakalar cin hanci da rashawa, hukuncin da ke matsayin irinsa na farko da aka yankewa wadanda suka rike manyan mukamai a kasar.

Talla

Ka zalika wannan ne shari’ar ita ce irinta ta farko da ke biyo bayan murabus din shugaba Abdelaziz Bouteflika da ya yi murabus daga mulkin kasar bayan tsanatar zanga-zangar adawa da gwamnati.

Cikin wadanda aka yankewa hukuncin na yau har da Ahmed Ouyahia wanda zai shafe shekaru 15 a gidan yari yayinda Abdelmalek Sellal zai shafe shekaru 12

Tun bayan samun ‘yanci daga hannun Faransa a shekarar 1962 wannan ne karon farko da Firaminista zai dandani zaman yari a Algeria.

Masu shigar da kara dais un bukaci kotu ta yankewa mutanen 2 shekaru 20 a gidan yari ne, amma kuma kotun ta sassauta hukuncin zuwa shekaru 15 da 12.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI