Najeriya-Lagos

'Yan sanda a Lagos sun kame daruruwan 'yan Okada

'Yan Okada a Jihar Lagos Tarayyar Najeriya
'Yan Okada a Jihar Lagos Tarayyar Najeriya

Jami’an tsaro sun kaddamar da samame tare da kame daruruwan ‘yan Okada a jihar Lagos da ke Najeriya, inda wasu bayanai ke cewa jami’an tsaron kan afka wa ‘yan okodan a inda suke kwana domin kwashe mutane da Babura.

Talla

Bayan sumamen Jami'an 'yansandan na baya-bayan nan kan Baburan masu sana'ar ta Acaba ko kuma Okada galibi 'yan Arewa, Sashen Hausa na Radio France RFI ya nemi ji daga bakin rundunar inda kakakinta Bala Elkana ke cewa matakin ya biyo bayan bincikensu da ke nuna cewa 'yan Okadan ne ke haddasa cunkoso a jihar Lagos.

A cewar Bala Elkana ta hakane kadai za su magance matsalar cunkoson ababen hawa da ya addabi jihar, ko dai bai yi gamsasshen bayani kan makomar baburan da suka kame ba.

A bangare guda yayin taron manema labaran hadin guiwa da kungiyar ‘yan Okodan da kuma shugabannin ‘yan arewacin Najeriya, suka gudanar jiya litinin a birnin na Lagos, sun bukaci a kawo karshen wannan kame da suka ce ya saba wa ka’ida.

Shetima Yerima, daya daga cikin wadanda suka jagoranci taron manema labaran ya yi wa Abdoulkarim Ibrahim Shikal karin bayani a game da wannan matsala.

'Yan sanda a Lagos sun kame daruruwan 'yan Okada

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI