'Yan ta'adda sun kashe mutane a otel din Somalia
Wallafawa ranar:
Akalla mutane biyar sun rasa rayukansu a wani harin da mayakan jihadi suka kaddamar kan wani otel da ke babban birnin Mogadishu na Somalia kamar yadda jami’an ‘yan sanda suka tabbatar , yayin da rahotanni ke cewa, an yi nasarar hallaka daukacin maharan bayan dauki-ba-dadin da aka yi da su na tsawon sa’o’i.
Kungiyar al-Shebab ta dauki alhakin harin wanda aka kai kan ote din SYL wanda fitattun ‘yan siyasa da manyan sojoji da jami’an diflomasiya ke yawan zama a ciki.
Sanarwar da rundunar ‘yan sanda ta fitar, ta ce, jami’anta sun kawo karshen tashin hankalin, inda kuma suka kubutar da mutane sama da 80 da suka hada da jami’an gwamnati.
Jami’an tsaro biyu da fararen hula uku sun rasa rayukansu a harin na ta’addanci , yayin da sojoji biyu da fararen hula tara suka jikkata.
Shaidu sun rawaito cewa, maharan sun yi shigar burtu, inda suka sanya kakin ‘yan sanda, abin da ya ba su damar kusantar otel din cikin sauki tare da bude wuta kan mai uwa da wabi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu