INEC

Jami'an INEC 2 za su yi zaman yarin shekaru 21 kan karbar na goro

Wasu jami'an hukumar zaben Najeriya INEC.
Wasu jami'an hukumar zaben Najeriya INEC. STEFAN HEUNIS / AFP

Wata kotu a birnin Yola na jihar Adamawa ta daure wasu jami’an hukumar zaben Najeriya guda 2 shekaru 21 a gidan yari, saboda samun su da laifin karbar cin hancin kudin da ya kai naira miliyan 362 daga hannun tsohuwar ministan albarkatun man kasar, Diezani Allison Madueke lokacin zaben shekarar 2015.

Talla

Jaridar ta ce mutanen da kotun ta samu da laifi sun hada da Ibrahim Mohammed da Sahabo Iya-Hamman bayan alkali Nathan Musa ya amince da shaidu 15 da EFCC ta gabatar dangane da tuhumar da ake musu.

Jaridar ta ce alkali Musa ya bukaci Sufeto Janar na 'yan Sandan Najeriya Muhammadu Adamu da ya hada kai da rundunar Yan Sandan duniya domin kamo tsohuwar ministar dan ganin ita ma ta fuskanci hukunci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI