Algeria

Zanga-zanga ta haddasa matsala ga zaben Algeria

Masu zanga-zangar adawa da zaben Algeria.
Masu zanga-zangar adawa da zaben Algeria. REUTERS/Ramzi Boudina

Al’ummar Algeria na ci gaba da kada kuri’a a zaben shugaban kasa dai dai lokacin da zaben ke fuskantar zanga-zangar adawa daga masu fafutukar ganin an gudanar da shi bisa tsari, matakin da ya kai ga kamen tarin jama’a a rumfunan zabe wadanda mahukuntan kasar suka zarga da yunkurin tayar da zaune tsaye.

Talla

Dubban masu zanga-zangar wadanda su ne musabbabin murabus din tsohon shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika sun kalubalanci matakin fitowa zaben a yau Alhamis inda suka sake jan daaga a manyan titunan kasar, ciki har da wadanda suka tarwatsa rumfunan zabe tare da kwashe kayakin aikin zaben na Algeria.

Wasu shaidun gani da ido sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa wasu tarin matasa sun farwa rumfunan zabe a yankin Kabylie jim kadan bayan bude rumfunan a safiyar yau Alhamis.

Shaidun sun kuma bayyana yadda jami’an tsaro suka kame tarin matasan a yankin na Kabylie da biranen Tizi Ouzou da kuma Bouira wadanda ke kalubalantar zaben tare da neman lallai a gudanar da wasu gyare-gyare a manyan mukaman kasar.

Yankin Kabylie na arewacin Algeria ya yi kaurin suna wajen adawa da shirye-shiryen gwamnati inda zanga-zangar adawa tafi tsananta a yankin.

‘Yan takara 5 ne dai ke karawa a zaben na yau don neman kujerar shugabancin kasarta Algeria ciki kuwa har da mutum 3 da masu zanga-zangar suka fi kalubalanta bisa kafa hujja da cewa ‘ya’yan gwamnatin da ta gaba ne ciki har da tsaffin Firaminista 2, Abdelmajid Tebboune da Ali Benflis sai kuma tsohon minista Azzedine Mihoubi.

Zaben na yau wanda dama ba a saran fitowar jama’a ba, ana saran kulle rumfunan zabe da karfe 6 na yammacin yau, ko da dai ba a tsammanin sanar da sakamakon zaben a gobe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI