Najeriya

Najeriya na asarar miliyan 600 duk wata a tashoshin fitar da kaya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. REUTERS/Siphiwe Sibeko

Gwamnatin Najeriya ta ce tana asarar kudin da ya kai Naira miliyan 600 kowanne wata sakamakon tsaikon da motocin dakon kaya ke fuskanta a hanyar shiga da fita tashoshin jiragen ruwan kasar.

Talla

Dan Majalisar wakilai Victor Akinjo ya sanar da haka, yayin da ya ziyarci tashar jiragen ruwan Warri, daya daga cikin tashoshin da ake amfani da su wajen shigar da kaya kasar.

Akinjo ya ce ganawar da suka yi da masu ruwa da tsaki a Tashoshin shigar da kaya kasar ya ce matsalar sufuri wajen daukar kaya da kuma fitar da su na iya yin gagarumar illa ga tattalin arzikin Najeriyar, wanda ke bukatar daukar matakan gagagwa akai.

A watanni baya, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bai wa mataimakin sa farfesa Yemi Osinbajo umarnin daukar mataki akai, abinda ya kai ga rage wahalar da ake fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI