Afrika

An fara makokin Sojin Nijar 71 da 'yan ta'adda suka kashe

Fadar shugaban jamhuriyar Nijar ta sanar da zaman makoki na tsawon kwanaki uku daga yau juma’a, don nuna alhini dangane da harin da ‘yan ta’adda suka kai a garin Inates tare da kashe sojojin kasar 71.

Gawarwakin sojojin da suka rasa rayukansu a Inates da aka iso da su birnin Yamai
Gawarwakin sojojin da suka rasa rayukansu a Inates da aka iso da su birnin Yamai RFI-HAUSA
Talla

A yau juma’a za aka isa da gawarwakin sojojin da suka rasa rayukansu a birnin Yamai don yi masu jana’izar karramawa, yayin da majalisar dokokin kasar ta yi zama na musamman dangane da wannan lamari.

Kungiyoyin farraren hula sun bukaci hukumomin kasar da yan siyasa sun hda karfi don shawo kan wannan matsala.

An bayyana cewa yan kasar da dama ne suka nuna rashin gamsuwar su ganin siyasar da gwamnatin kasar ta Nijar ke takawa dangane da zancen tsaro a wasu sassan kasar a wannan yaki da yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI