Algeria

Sabon shugaban Algeria ya nemi zama da masu zanga-zanga

Sabon shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune.
Sabon shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune. REUTERS/Ramzi Boudina

Sabon shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune ya sha alwashin bayar da cikakkiyar dama ga matasan da ke zanga-zangar neman sauyi wajen ganin sun shigo don a dama da su wajen ciyar da kasar gaba.

Talla

A cewar shugaban wanda ya samu nasara a zaben kasar na jiya Alhamis da gagarumin rinjaye, kofa a bude ta ke ga masu zanga-zangar don zaunawa da sabuwar gwamnati tare da fayyace bukatunsu.

Tun cikin watan Fabarairun da ya gabata ne, Algeria ke fuskantar zanga-zangar juyin juya hali da ta yi awon gaba da kujerar shugaban kasar da ya gabata Abdelaziz Bouteflika, zanga-zangar da daga bisani ta kalubalanci zaben kasar tare da neman lallai a ruguje ilahirin mukaman gwamnati.

Cikin wani taron manema labarai da Tebboune wanda tsohon Firaministan kasar ta Algeria yak ira bayan sanar da shi a matsayin mai nasara a zaben da rinjayen kashi 58 cikin 100 na yawan kuri’un da aka kada, ya ce yana maraba da duk wani bangare da zai hada hannu wajen ciyar da kasar gaba.

Dattijon sabon shugaban kasar ta Algeria mai shekaru 74 wanda ko akan hanyar zuwa taron manema labaran na yau sai da ya sha ruwan duwatsu ya ce a shirye ya ke ya samarwa al’ummar Algeria sauyin da su ke bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI