Wasanni

Ya dace Platini ya mayarwa Fifa da kudadden ta

Michel Platini, a shelkwatar FIFA  dake Zurich a Switzerland
Michel Platini, a shelkwatar FIFA dake Zurich a Switzerland uefa

Hukumar kwallon kafa ta Duniya Fifa ta bukaci tsohon Shugaban hukumar kwallon kafar Turai Michel Platini da ya dawo da wasu kudaddeda hukumar ta zuba masa a lokacin Shugabanci Sepp Blatter mutumen da aka haramta masa shiga zantukan da suka jibanci harakokin kwallon kafa a Duniya na wani lokaci.

Talla

Michel Platini, Mutumen da hukumar Fifa ke bukatar ganin ya mayar da wasu kudadde da aka kiyasta yawan su da milyan biyu na kudin kasar Swizilland da aka kiyasta su a Euros milyan daya da dubu 84 da ka zuba masa a lokacin shugabancin tsohon Shugaban hukumar Fifa Sepp Blatter.

Karbar wadanan kudade ya janyowa Michel Platini dakatarwa na tsawon shekaru 4.

Michel Platini ya bayyana cewa,karbar wadanan kudadde bai sabawa dokkokin hukumar ta Fifa ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI