An gudanar da Jana'izar sojojin Nijar da yan ta'adda suka kashe a harin Inates

Sauti 21:05
Gawarwakin sojojin da suka rasa rayukansu a Inates da aka iso da su birnin Yamai
Gawarwakin sojojin da suka rasa rayukansu a Inates da aka iso da su birnin Yamai RFI-HAUSA

A jamhuriyar Nijar ranar juma’a 13 ga watan Disemban nan ne aka yi jana’izar sojojin kasar 71 da suka rasa rayukansu sakamakon harin ta’addanci a barikinsu da ke Inates kusa da iyakar kasar da Mali.An yi jana’izar ne a cikin barikin sojiin saman kasar da ke birnin Yamai karkashin jagorancin shugaba Issifou Mahamadou da kuma jami’an diflomasiyar kasashen ketare.Bashir Ibrahim a cikin shirin mu zagaya Duniya ya mayar da hankali tareda duba wasu daga cikin manyan labaren Duniya.