Libya

Kasashen Duniya na ci gaba da kira don ganin an kawo karshen yakin Libya

Dakarun janar Haftar a wani yanki daf birnin Tripoli
Dakarun janar Haftar a wani yanki daf birnin Tripoli Reuters/ Esam Omran Al-Fetori

Kasashen Faransa, Jamus da Italiya a jiya juma’a sun bukaci ganin an kawo karshen gumurzu tsakanin dakarun Janar Haftar da sojojin gwamnatin hadin kan Tripoli dake samun goyan bayan kasashen Duniya.

Talla

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, Uwargida Angela Merkel daga Jamus da Shugaban gwamantin Italiya Guiseppe Conte a wata sanarwa ta hadin gwuiwa sun gayyacin bangarorin dake fada da juna da su kawo karshen yakin.

Shugabanin sun bayyana cewa suna a shirye don kawo shawwarwari tareda hadin gwuiwar kungiyar kasashen Afrika ta AU da majalisar dimkin Duniya don ganin an lalubo hanyoyin tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasar ta Libya, yayinda janar Haftar ke ci gaba da bayyana aniyar sa ta afkawa birnin Tripoli cibiyar gwamnatin hadin kan kasar .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.