Sudan

Kotu ta daure tsohon shugaban Sudan

Kotu a Sudan ta zartas da hukuncin daurin shekaru 2 kan tsohon shugaban kasar Oumar al-Bashir, bayan tabbatar da laifin cin hanci da rashawar da ake tuhumarsa da aikata.

Tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir.
Tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan al-Bashir. Reuters
Talla

Za dai a tsare tsohon shugaba al-Bashir ne a wata cibiyar gyaran halayyar wadanda aka kama da laifukan cin hancin.

Kotu ta samu tsohon shugaban na Sudan ne da laifin boye miliyoyin kudaden kasashen ketare a gidansa, laifin da alkali Sadiq AbdelRahman ya ce na tattare da hukuncin daurin akalla shekaru 10.

Sai dai saboda shekarun tsohon shugaban 75, alkalin ya sassauta hukuncin zuwa daurin shekaru 2.

A watan Afrilun da ya gabata, sojoji suka kawo karshen gwamnatin al-Bashir, bayan shafe watanni dubban ‘yan kasar na zanga-zangar neman tilasta masa yin murabus, bayan shafe kusan shekaru 30 yana mulkin Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI