ECOWAS - Saliyo

Kotun ECOWAS ta soke dokar hana masu juna biyu zuwa makaranta

Wasu 'yan mata dalibai akan hanyarsu ta zuwa gida daga makaranta Saliyo.
Wasu 'yan mata dalibai akan hanyarsu ta zuwa gida daga makaranta Saliyo. REUTERS/Cooper Inveen

Babbar Kotun Afrika ta Yamma dake zamanta a Najeriya, ta baiwa gwamnatin Saliyo umarnin janye dokar haramtawa 'yan mata dalibai da suka samu juna biyu halartar makarantu, matakin da kungiyoyin kare hakkin ke fatan zai share fagen kalubalantar irin dokar a wasu kasashen nahiyar ta Afrika.

Talla

A shekarar 2015, Gwamnatin Saliyo ta kafa dokar, bisa hujjar cewa, kyale 'yan matan da suke da juna 2 halartar makaranta, zai wahalar da su, jawo musu tsangwama da kuma karfafawa wasu yaran mata kokarin samun juna biyun.

Bayan kafa dokar ce, gwamnatin Saliyo ta kafa wasu cibiyoyi a sassan kasar, inda aka tsarawa yara matan masu juna biyu daukar karatu a lokuta kayyadaddu, sai dai babbar kotun ECOWAS ta kasashen yammacin Afrika ta yi watsi da shirin, wanda tace ba zai kashe kishirwar ilimin dake damun yara matan ba.

Wata kididdiga ta nuna cewar nahiyar Afrika ke kan gaba a duniya wajen adadin 'yan mata dalibai dake samun juna 2, inda kasashe 18 a nahiyar suka kafa dokar tilasatawa yara matan fita daga makaranta muddin suka samun juna biyun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI