G5 Sahel

An soma taron kasashen G5 Sahel a Jamhuriyar Nijar

Shugabannin kasashen G5 Sahel yayin jimamin dakarun Nijar 71 da mayaka suka halaka.
Shugabannin kasashen G5 Sahel yayin jimamin dakarun Nijar 71 da mayaka suka halaka. RFIHAUSA/Kubura Illo

Shugabannin Kasashen dake cikin rundunar G5 Sahel dake yaki da Yan ta’adda na gudanar da wani taro a Birnin Yammai dake Jamhuriyar Nijar, bayan kazamin harin da ya lakume rayukan sojojin kasar 71 a sansanin su dake kusa da iyakar Mali.

Talla

Cikin shugabannin da suka isa birnin Yammai yau sun hada da shugaba Idris Deby na Chadi da Ibrahim Boubacar Keita na Mali da shugabannin Burkina Faso da kuma Mauritania.

A ranar juma’ar da ta gabata aka gudanar da bikin jana’iza ta kasa domin karrama sojojin 71 da suka sadaukar da rayukan su wajen kare kasa.

Tuni kungiyar IS ta dauki alhakin kazamin harin, wanda shine irin sa mafi muni da aka taba kaiwa sojojin Nijar, a karkashin yaki da Yan ta’addan da kasar keyi.

Wannan hari ya sa shugaba Emmanuel Macron ya dage taron da ya shirya gudanarwa da shugabannin kasashen an kungiyar G5 Sahel a garin Pau domin sake Nazarin matsalar tsaron da ya addabi yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI