Afrika

Shugaba Keita ya jagoranci taron zaman lafiya kasar Mali

Ibrahim Boubacar Keïta Shugaban kasar Mali a zauren taron zaman lafiya a Bamako
Ibrahim Boubacar Keïta Shugaban kasar Mali a zauren taron zaman lafiya a Bamako Capture d'écran

Shugaban Mali Ibrahim Boubacar Keita, a jiya asabar ya jagoranci taron zaman lafiyar kasar,Shugaban na Mali ya gayyaci daukacin kungiyoyin farraren hula na kasar, yan siyasa, da kungiyoyi dake dauke da makamai.

Talla

Jam’iyoyin adawa sun kauracewa zaman taron da aka soma jiya a babban birnin kasar Bamako, inda aka bayyana akalla mutane dubu uku a zauren taron.

Taron, yunkurin ne na gwamnatin Mali wajen amfani da tattaunawar sulhu, don kawo karshe tashe-tashen hankula a sassan kasar na hare-haren masu ikirarin Jihadi, da rikicin kabilanci.

An dai soma tattaunawar zaman lafiyar ne watanni bayan fuskantar tashin hankalin a wasu yankunan kasar Malin wacce ta fuskanci hare-hare daga kungiyoyin yan ta’adda, abinda yayi sanadin salwantar rayukan dakarun kasar sama da 140.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.