Amurka ta soki shugabannin Afrika kan gaza yakar ta'addanci
Wallafawa ranar:
Kasar Amurka ta soki shugabannin kasashen Afirka ta Yamma da gazawa wajen yaki da 'yan ta’addan da suka addabi yankin.
Yayin gudanar da wani taro na musamman kan halin da ake ciki a Yankin Sahel, Jakadiyar Amurka Cherith Norman ta shaidawa kwamitin sulhu cewar shugabannin kasashen dake Yankin basa daukar matakan da suka dace wajen yakin dake gaban su.
Cherith tace daukar matakan soji kawai ba zai magance matsalar da ta haifar da tashin hankali a yankin ba, inda take cewa Amurka ta bada taimakon da ya kai Dala biliyan 5 da rabi daga shekarar 2017 zuwa 2018 domin samar da tsaro a Afirka ta Yamma.
Jami’ar ta bayyana kasar Mali a matsayin wadda ta kasa samun cigaba wajen samar da zaman lafiya duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a shekarar 2015.
Norman tace yana da muhimmanci kasashen dake Afirka ta Yamma da su baiwa kowanne bangare damar fada aji kan shugabancin kasashen su da kuma raba arzikin kasa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu